News
Tunanin ’Yan Boko Ne Ke Cewa N5,000 Da Gwamnatin Tarayya Take Ba Wa Talakawa Ta Yi Kadan – Minista Sadiya

Daga kabiru basiru fulatan
Sadiya ta bayyana haka ne bayan an yi mata tambaya game da amfanin da N5,000 da gwamnati ke ba wa talakawa a duk wata a yunkurinta na fitar da ’yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci.
A cewarta, ma’aikatar da take jagoranta ganau ce kan yadda N5,000 din da ake biyan talakawa masu rauni a wata-wata ke taimakawa wajen fitar da su daga matsanancin talauci.
Hajiya Sadiya ta ce idan aka lura, mutanen da aka ba wa N5,000 din tana da matukar muhimmacni a gare su, domin talakawa ne masu rauni, kuma tana kyautata musu rayuwa