Connect with us

Sports

Antonio Conte ya ce tawagar Tottenham ba tada karfi kamar da

Published

on

123286676 antonioconteanddelealli.jpg
Spread the love

Daga muhmmad muhmmad zahraddin

Kocin Tottenham, Antonio Conte ya ce tawagarsa ta rage karfi a kasuwar musayar ‘yan kwallo a watan Janairu duk da cewa sun sayi ‘yan wasa biyu.

Spurs ta dauko ‘yan wasa biyu daga Juventus Dejan Kulusevski da Rodrigo Bentancur amma sai ta bayar da aron Tanguy Ndombele da kuma Giovani lo Celso.

Advertisement

Sannan Dele Alli ya koma Everton a yayin da Bryan Gil ya koma taka leda a Valencia.

“Abin da ya faru a cikin watan Janairu babu sauki,” Conte ya shaidawa tashar Sky Sport Italia.

Ya kara da cewa “Mun rasa manyan ‘yan wasanmu hudu a Tottenham sai muka siyo guda biyu”.

Advertisement

“Ko a yawa mun ragu a maimakon karawa tawagarmu karfi.”

Conte ya koma Tottenham ne a ranar 2 ga watan Nuwambar 2021.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *