Sports
AC Milan da Juventus na zawarcin Depay, Vazquez zai bar Madrid
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Har yanzu Arsenal na sha’awar sayen dan wasan gaba na Spain Alvaro Morata, mai shekara 29 wanda ke zaman aro (Calciomercato)
Kocin Manchester City Pep Guardiola yana son kungiyar ta tsawaita kwantiragin dan wasan gaban Ingila Raheem Sterling, mai shekara 27. (Fabrizio Romanor).
Houston Dynamo ta yi tayin sayen dan wasan tsakiya na Atletico Madrid da Mexico Hector Herrera, mai shekara 31. (MLS)
Dan wasan gefe na Real Madrid Lucas Vazquez, mai shekara 30, yana son barin kungiyar don ya kasance cikin tawagar Spain a gasar cin kofin duniya. (El Nacional, in Spanish)
Ƙungiyoyin Italiya uku Inter Milan da AC Milan da Juventus na zawarcin dan wasan gaban Barcelona da Netherlands Memphis Depay, mai shekara 28. (Sport, in Spanish)
Tottenham ce ke kan gaba wajen neman dan wasan bayan Inter Milan da Netherlands Stefan de Vrij, mai shekara 30. (InterLive, via Star)
Everton na iya kokarin siyan daya daga cikin ‘yan wasan Chelsea uku da ba aron aro na Billy Gilmour, Conor Gallagher ko Armando Broja a bazara.
Dan wasan tsakiyar na Scotland Gilmour, mai shekara 20, yana Norwich, shi kuma dan wasan tsakiya na Ingila Gallagher, mai shekara 22, yana Crystal Palace, yayin da shi kuma dan wasan Albania Broja, mai shekara 20, yana Southampton. (Givemesport)
-
Opinion7 days ago
Ayyuka, Bin Diddigi, Biyan Kudi, Sakamako: Dabarun Kano Da Suka Zarce Jihohi 35
-
Opinion7 days ago
Tiriliyan ₦210 na Karya: Yadda Bala Wunti Ya Warware Dukkan Rudanin da Ya Mamaye Zaman Majalisar Dattawa Kan Asusun NNPC
-
News5 days ago
Likitan El-Rufai Ya Shiga Matsala Kan Zargin Bayar Da Rahoton Jinya Na Bogi
