Connect with us

Sports

Kano Pillars ta farfado bayan doke Abia Worriors 2-1

Published

on

Kano Pillars
Spread the love

Daga kabiru basiru fulatan

 

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta doke Abia Worriors 2-1 a filin Ahmadu Bello da ke garin Kaduna.

Abia Worriors ne suka fara saka kwallo a minti na 16 da fara wasa, daga nan kuma Pillars ta farke ta kuma kara ta hannun Saidu Salisu da kuma Abdullahi Musa.

Advertisement

Duk da haka a yanzu masu gida na na 14 ne a teburi da maki 17.

Ganin cewa filin Kano Pillars na bukatar gyara hakan yasa ta mayar da Kaduna a matsayin gidanta na wani lokaci.

To amma magoya bayan kungiyar na ci gaba da kira ga gwamnatin jihar Kano da ta mayar da hankali wurin ganin ta gyara filin wasan na Pillars don su rika wasa a gida.

Advertisement

A mako mai zuwa Pillars za su je bakunta birnin Enugu don karawa da Enugu Rangers, kafin su kuma su karbi bakuncin Rivers United mako daya bayan sun dawo.

Sai dai Katsina United mai makwabtaka kunnen doki ta tashi 1-1 a gidanta da Heartland, yayin da Lobi Stars ta doke Remo Stars 1-0.

Sai kuma Nassarawa United da ita ma 1-0 ta ci Niger Tornadoes a birnin Lafiya.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *