News
Banga abin da PDP ko APC za suyi talla da shi a 2023 ba – Kwankwaso
Daga muhmmad muhmmad zahraddin
Tsohon Gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa ya ce babu wani abu da jami’iyyun APC da PDP zasu nunawa al’umma domin yakin neman zabe a shekarar 2023.
Sanata Kwankwaso ya bayyana hakan ne ta cikin shirin “Akida da Gaskiya na gidan rediyon Nasara da ke Kano.
Hakan na zuwa ne bayan da wasu rahotanni suka bayyana Kwankwaso na shirin barin PDP.
“Ya ce, “Ni banga wani abu da zance APC Ko PDP ka iya nunawa a zaben 2023 domin samun goyan bayan ‘yan kasar nan ba,”
“Wanda nake gani abin da ya fi da cewa shi ne al’umma suyi duba na tsanaki wajen marawa jami’iyyar da zata fito da su daga halin kunci da suke a yanzu,” a cewar Kwankwaso.
Tsohon Gwamna Kwankwaso na cikin manyan jiga-jigan jam’iyyar PDP na ƙasa, kuma shi ne jagoranta a Kano.
Kwankwaso ya nemi takarar shugaban ƙasa a zaɓen da ya gabata amma bai yi nasara ba tun a zaɓen fitar da gwani.