News
NDLEA ta kama wani mutum da Jabun dala miliyan 4 da dubu dari 7.
Daga kabiru basiru fulatan
Hukumar hana sha da fataucin muyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta kama wani mutum mai suna Abdulmumini Maikasuwa da Jabun kudaden Amurka (dollars) da suka kai dala miliyan hudu da dubu dari bakwai da sittin kwatankwacin Naira biliyan biyu da miliyan dari bakwai.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar ta NDLEA Mista Femi Babafemi, ya ce an kama mutumin ne a garin Abaji dake birnin tarayya Abuja lokacin da mutumin ke kokarin fara kashe kudin.
A cewar sa mutumin ya taho da kudaden ne daga Lagos.