Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta saka ranar 26 ga watan Maris don gudanar da babban taronta na ƙasa.
Mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Salisu Na’inna Dambatta, ya faɗa BBC Hausa cewa za a gudanar da taron ne a Abuja.
Jam’iyyar ta cimma matsayar ne jim kaɗan bayan ta sanar da fasa gudanar da shi ranar 26 ga Fabarairu.
Jaridar indaranka ta fahimci cewa yanzu haka mambobin kwamatin riƙo na shugabancin APC ƙarƙashin Gwamna Mai Mala Buni suna ganawar sirri.
Tun farko APC ta sanar da hukumar zaɓe ta INEC cewa za ta gudanar da tarukan shiyya kafin na ƙasa baki ɗaya.