Connect with us

News

Yajin Aiki: Gwamnatin Nijeriya za ta gana da ASUU a yau Talata

Published

on

FB IMG 1645506689429
Spread the love

Daga kabiru basiru fulatan

 

 

Da alama dai yajin aikin gargaɗi da Ƙungiyar Malaman Jami’a ta Ƙasa, ASUU ta fara ba zai kai wata ɗaya kamar yadda ta ɗauki aniya ba, bayan da Gwamnatin Nijeriya ta yi wuf ta fara yunƙurin daƙile wannan mataki na ƙungiyar.

Advertisement

Tuni ma dai gwamnatin, ta bakin Charles Akpan, Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a da Labarai na Ma’aikatar Ƙwadago da Ɗaukar Aiki, ya baiyana a yau Litinin a wata sanarwa.

Ya ce Ministan Ƙwadago da Ɗaukar Aiki, Chris Ngige ne zai gana da shugabannin ASUU ɗin da wasu masu ruwa da tsaki a ma’aikatun gwamnati.

Ya ce za a yi ganawar ne a yau Talata da ƙarfe 1 na rana a ofishin Ministan.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *