News
APC ta sanya sabuwar ranar da za ta yi babban taro

Daga yasir sani abdullahi
Kwamitin Riƙo na Jam’iya mai mulki ta APC ya sanya 26 ga watan Maris a matsayin ranar babban taro na jam’iyar.
John Akpankudohede, Sakataren jam’iyar na ƙasa, shi ne ya baiyana hakan ga manema labarai jin kaɗan bayan wata ganawar sirri a Abuja a jiya Litinin.
Akpankudohede ya ce bayan da a ka tattauna, Kwamitin Riƙo na jam’iyar ya sahale cewa tun ranar 24 ga watan Febrairu za a fara shirye-shiryen taron inda zai ƙare a ranar 26 ga watan Maris a filin Eagles Square.
Ya kuma ƙara da cewa kafin babban taron, jam’iyar ta amince da yin taruka na shiyya-shiyya.
Ya kuma ce za a bi tsare-tsare da jadawalin lokaci da jam’iyar ta tsara wajen aiwatar da taron.