News
Martanin da matasan Najeriya suka mayar wa Tinubu kan kalamansa a kansu

Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Matasa da dama a Najeriya sun bazama a shafukan sada zumunta inda suka dinga mayar wa jagoran jam’iyya mai mulki ta APC Bola Ahmad Tinubu martani, kan kalamansa da ya yi a kansu, cewa za su yi shugabancin ƙasa amma sai bayan ya yi.
Tsohon gwamnan Legas kuma wanda ya ayyana aniyarsa ta tsaya wa takarar shugaban ƙasar Najeriya ya faɗi hakan ne a ziyarar da ya kai wa Alaafin na Oyo Lamidi Adeyemi, a ranar Lahadi.
Tinubu ya buƙaci matasa su ba magabatansu dama.
An ambato Tinubun na cewa: “Kun toshe wa magabatanku dama tun kafin ku zama shugaban ƙasa, idan kun zama shugaban ƙasa fa, za ku kore mu ne a gari? Sai kun tsufa za ku zama shugaban ƙasa, kuma sai na riga zama shugaban ƙasa.”
Matasa a Najeriya sun daɗe suna fafutikar ganin sun kai ga madafan iko, da samun muƙaman siyasa, kuma suna ƙorafin cewa dattijai sun hana su rawar gaban hantsi tuntuni.
Waɗannan kalamai na Tinubu sun hargitsa matasa inda suka yi ta mayar da martani a kafefen sada zumunta a ranar Litinin.
“Idan kana goyon bayan Tinubu to aƙidarku iri ɗaya. Babu wanda zai faɗi haka idan yana son ci gaban ƙasarsa. Ba ma ya tunanin maganar kafin ya faɗe ta. Tinubu kan sa kaɗai ya sani, duk abin da ba zai amfane shi ba shirme ne,” a cewar wani mai suna @CalebsLeke a Twitter.
A shafin Twitter an yi ambaci sunan Tinubu kusan sau 20,000, yayin da a Facebook kuma yake cikin maudu’ai masu tashe inda aka yi amfani da sunansa sama da sau 135,000.
Me matasan ke cewa?
Wani mai suna Muhammad Omar ya bayyana ra’ayinsa da cewa: “A gaskiya dattawan nan ku tsaya ku yi tunani, ku je gida ku huta, ku bar matasa su gwada himmarsu da kuma hazaƙarsu tare da basirar da Allah ya ba su. Amma idan ka ce haka to yaushe ne za a ba mu dama? Wani ma idan ya zo haka zai ce.”
Abubakar Umar Masha’Allahu-kana cewa ya yi: “Mu dai muna roƙon tsofaffin nan da su janye gefe su ba matasa dama tun da sun kasa samar wa ‘ƴan Najeriya wuta da ruwa sama da shekara 55.”
Ma’abota shafin Twitter na BBC Hausa ma ba a bar su a baya ba, inda suka tofa albarkacin bakinsu sau 53 cikin awa biyu.
BBC News Hausa@bbchausa·2hTsohon gwamnan Legas kuma jagoran jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya faɗawa matasan ƙasar cewa za su yi shugabancin ƙasa amma sai bayan magabatansu sun yi.
Isa Mousa (@IsaMousah) ya ce “waɗannan magabatan ba za su taɓa gamawa ba. 🙄😏”.
Sai kuma Auwal Dabai Unguwa uku (@AuwalunDabai) da ya ce: “Allah ne mai ikon komai da komai, Kuma Mai ba da mulki ga wanda ya so a lokacin da ya so.”
Na shafe tsawon rayuwata ina fatan zama shugaban ƙasa – Tinubu
A ranar 10 ga watan Janairu tsohon gwamnan Legas ɗin ya ce ya faɗa wa Shugaba Muhammadu Buhari aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin ƙasar a babban zaɓe na 2023.
Ya bayyana hakan ne a fadar shugaban ƙasa bayan wata ganawa da Buhari a birnin Abuja.
A cewar Tinubu: “Na faɗa wa Shugaba Buhari aniyata, ban ji abin da ba shi na yi tsammanin ji daga gare shi ba. Ya ƙarfafa min gwiwa kamar yadda dimokuraɗiyya ta ba ni dama, amma har yanzu ban sanar da jama’ar Najeriya ba tukunna, ina ci gaba da tuntuɓa.
“Na shafe tsawon rayuwata ina fatan zama shugaban ƙasa, don haka me ya sa zan yi tsammanin jin abin da ya saɓa da wannan daga wajensa. Tsari muke bi da dimokuraɗiyya, don haka dole mu tafi a kan haka.”
Da ma an daɗe ana raɗe-raɗin zai yi takarar amma ya ja bakinsa ya yi gum, kafin ya bayyana hakan a farkon shekarar 2022.
Sai dai wasu ‘yan takara daga ɓangaren kudu maso gabashin Najeriya, inda ƙabilar Igbo suka fi rinjaye, sun yi alwashin ƙalubalantarsa a zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar.
Sanata Orji Uzor Kalu da Gwamnan Jihar Ebonyi David Umahi da Sanata Rochas Okorocha na cikin waɗanda suka bayyana sha’awarsu ta neman shugabancin Najeriya a ƙarƙashin APC mai mulki yayin da Buhari zai kammala wa’adinsa na biyu a watan Mayun 2023.