News
KOTU TA CE ATIKU ‘DAN NIGERIA NE YANA DA ‘YANCIN TSAYAWA TAKARA.

Daga aminu usman jibrin
Wata babbar kotun tarayya dake Abuja tayi watsi da karar da aka shigar gabanta ana kalubalantar ‘yancin da tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar na tsayawa takarar shugaban kasa.
Tun farko wata kungiya ce da ke rajin kare mulkin dimukuradiya a Kasar nan ta shigar da karar tana kalubalantar ‘yancin da Atiku ke dashi na neman mulkin kasar nan saboda ba a haifeshi a Nigeria ba.
A cewar kotun tun farko wadanda ya shigar da karar basu da ‘yancin yin hakan.