Connect with us

Sports

Newcastle ta shirya daukar Zaidu Sanusi, Man United na son Ndidi

Published

on

downloadfile
Spread the love

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

 

Newcastle za ta sake neman mai tsaron bayan Najeriya Zaidu Sanusi da ke wasa a FC Porto.

Jaridar ‘A Bola’ ta Focugal ta ruwaito cewa Magpies sun nemi dan wasan a watan Janairu amma sun kasa kai karshen ciniki da FC Porto.

Advertisement

Kazalika kungiyar ta tura tawagar masu sa’ido sun sake kallon salon taka ledar matashin, a wasan Europa da kungiyar ta yi da Lazio makon da ya wuce.

Zaidu Sanusi ya je Porto ne daga Santa Clara a 2020, kuma yana cikin tawagar Super Eagles da ta wakilci Najeriya a gasar cin kofin nahiyar Afrika ta AFCON da aka kammala a Kamaru.

Newcastle ta kashe kusan miliyan 100 wurin sayen yan wasa a watan Janairu, biyo bayan saye kungiyar da kamfanin Saudiyya karkashin Yarima Muhammad Bin Salman ya yi.

Advertisement

A wata mai kama da haka jaridar ‘Insider’ ta ruwaito cewa Leicester na shirin gabatar wa da Wilfred Ndidi sabuwar kwantiragi don ci gaba da rike mata tsakiya.

Dama kwantiragin Ndidi da Leicester za ta kare ne a karshen kakar 2024.

To amma kungiyoyin Firimiya kamar Aston Villa da Manchester United na shirin zuba miliyoyin fama famai, don jan ra’ayin Ndidi ya bar Leicester city bana.

Advertisement

Ba a jima ba da Aston Villa ta ce za ta biya fam miliyan 50 kan Ndidi a karshen kaka, to amma kocin Leicester Brendan Rodgers ya ce dan wasan tsakiyar ya haura haka.

Kawo yanzu dan Najeriyar ya buga wa kungiyarsa tasa wasa 201.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *