Sports
Senegal ta gina filin kwallo kafa na kece reni a birnin Diamniadio

Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Senegal ta kaddamar da sabon filin kwallon kafa mai cin mutum 50,000 wanda aka bude da wasan sada zumunta da ya hada da tsofaffin yan wasan Afrika.
An gina filin ne a birnin Diamniadio kuma an saka wa filin suna tsohon Shugaban kasa Abdoulaye Wade, da ya yi mulki daga shekarar 2000 zuwa 2012.
Birnin yana da nisan kilomita 30 daga babban birnin kasar Dakar.
Bikin na zuwa yan makonni bayan Senegal ta lashe gasar cin kofin nahiyar Afrika ta AFCON a Kamaru.
Tawagar Teranga Lions ta doke Egypt ne a bugun fenareti a wasan karshe a ranar 6 ga watan Fabrairu.
” A cikin wannan sabon fili da aka kawata za mu yi bikin mamaye Afrika a kwallon kafa da ma duniya baki daya.” In ji Shugaba Macky Sall.
Rahotanni sun ce filin wanda wani kamfanin Turkiyya ya gina ya lakume dala miliyan 270, kuma anan za a gudanar da Olympics na matasa a 2026.
Kazalika Shugaban Turkiyyar Recep Tayyip Erdogan ya halarci bikin, gabanin fara wasan sada zumunta da tsohon dan wasan Senegal Kalilou Fadiga ya ci kwallon farko.
Fadiga na daga cikin tawagar Teranga Lions da ta kai zagayen quarter-finals a gasar cin kofin duniya ta 2022.
Tsohon dan gaban Liverpool El Hadj Diouf da Samuel Eto’o na Kamaru, da Didier Drogba na Ivory Coast, da tsohon dan wasan Ghana Asamoah Gyan da kuma tsohon dan wasan gaban Najeriya Daniel Amokachi na daga cikin tsofaffin yan wasan da suka buga wasan kaddamar da sabon filin.
Hakama bikin ya samu halartar tsohon dan wasan duniya kuma shugaban Liberia George Weah, da kuma shugabannin Guinea-Bissau. da Gambia da Rwanda da kuma Jamus.
A fagen tamaula kuma Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya Gianni Infantino da kuma takwaransa a Afrika Patrice Motsepe duk sun shedi bikin.