Sports
EUROPA: Barcelona Ta Yi Waje Da Napoli
Daga yasir sani abdullahi
Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta bi Napoli har gida ta lallasa ta da ci 4 da 2 a gaban magoya bayanta.
Da sakamakon wannan wasa da aka kara a daren ranar Alhamis dai, tuni Barcelona ta wuce zagaye na gaba a Gasar Europa.
Kungiyoyin biyu sun tashi 1 da 1 ne a wasan farko da suka gwabza a filin wasa na Barcelona, wato Nou Camp, da ke birnin Catalonia a kasar Spain.
Jordi Alba, Frenkie de Jong, Gerard Pique da kuma Pierre-Emerick Aubameyang ne suka ci wa Barcelona.
Insigne da Politano su ne suka ci wa Napoli kwallonta biyu.