News
Buhari ya sanya hannu kan sabuwar dokar zabe

Daga kabiru basiru fulatan
Buhari ya saka hannu kan dokar ne ranar Juma’a a yayin wani takaitaccen buki a fadarsa a gaban idon Shugaban majalisar dattawa da na majalisar wakilan kasar.
Da yake jawabi lokacin da yake sanya hannu kan dokar, shugaban ya bukaci ‘yan majalisar da su hanzarta yin gyara ga sashe na 84 na dokar wanda ya tanadi haramta wa masu rike da mukaman gwamnati jefa kuri’a a zaben shugabannin jam’iyya ko kuma na ‘yan takara.