Connect with us

News

Tsaftar Muhalli: Gwamnatin Kano za ta kai wani kamfani kotu

Published

on

FB IMG 1645851905166
Spread the love

Daga yasir sani abdullahi

 

 

Advertisement

Gwamnatin Jihar Kano ta ce za ta gurfanar da wani kamfanin sarrafa man girki a kotu sakamakon gaza ɗaukar matakan tsaftace man da ya ke sarrafawa, wanda hakan ya ke barazana ga lafiyar al’umma.

Kwamishinan Muhalli na Jihar Kano, Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya baiyana hakan bayan kammala tsaftar muhalli ta ƙarshen wata ta kasuwanni da Ma’aikatun Gwamnati, wanda a ke gudanarwa a duk juma’ar karshen wata a nan Kano.

Ya ce kwamitin ƙoli na tsaftar muhalli na jihar Kano ya ziyarci ƙananan masana’antu da ke sarrafa man girki a Unguwar Dakata da ke Ƙaramar Hukumar Nassarawa inda ya tarar da yawa da ga cikin su suna aiki a muhalli mai datti da kazanta.

Advertisement

Ya ƙara da cewa za su gurfanar da shugaban ɗaya da ga cikin kamfanonin a gaban kotu, sakamakon yadda aikin ya ke barazana ga lafiyar alumma.

Ya ce “kamfanonin suna aiki ba tare da bin dokar tsaftar muhalli ba. Wasu suna sarrafa gyaɗa, amma abin takaicin shi ne yadda gyaɗar ta ke a zube a ƙasa, masu aikin na takawa da takalmin da suke shiga bandaki da shi.

“Suna aiki Babu kayan kariya daga wari ko Kura ko datti ko wani Abu Mai kama da hakan duk da cewa hakan ka iya haifar da yaduwar cututtuka ga al’umma,” in ji shi.

Advertisement

Kwamishinan ya ce zasu tattauna da shugabannin kungiyar kasuwar yankin da ma masu ruwa da tsaki domin daukar matakin da ya da ce.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *