Connect with us

News

Baƙaƙen fata ƴan Afirka sun ce ana nuna masu wariya a iyakokin Ukraine

Published

on

FB IMG 1646027553177
Spread the love

 

‘Yan Afirka da ke kokarin tsere wa daga Ukraine na ƙorafin fuskantar wariya a kan iyakokin Ukraine zuwa cikin Tarayyar Turai.

Wata daliba ƴar Najeriya da ke karatun likitanci a wata jami’a a Kharkiv, ta ce ta yi tafiya na tsawon sa’a 11 cikin dare kafin ta isa garin, da ke kan iyaka da Poland da Ukraine.

Advertisement

Tace “Lokacin da na zo nan na ga baƙaƙen fata suna bacci a yashe a kan titi,”.

Ta ce jami’an tsaron kan iyaka sun shaida mata cewa dole sai ta jira ƴan Ukraine da sauran fararen fata sun wuce sannan za a bata dama ta tsallaka ta tsira da ran ta.

Ba ta iya tantance ko masu gadin kan iyakar na Ukraine ne ko kuma Poland ba.

Advertisement

Ta ce ta ga an cika motocin bas da mutane waɗanda ta bayyana fararen fata ne, da aka amince su tsallaka kan iyaka, yayin da kuma ake zaɓen baƙaƙen fata da suka yi layi suna jiran tsammani.

Ruqayya na ƙoƙarin shiga Warsaw ne domin samun jirgin da zai dawo da ita gida Najeriya domin tserewa daga yakin da ake a Ukraine.

Shima wani ɗan Najeriya mai suna Isaac ya ce tun wuraren ƙarfe 4.30 na safe ya isa kan iyakar, kuma ya ce an faɗa masa cewa sai ƴan Ukraine da ƴan Turkiya sun wuce kafin baƙaƙen fata su wuce.

Advertisement

Jami’an kula da kan iyakokin Poland sun ce suna barin duk wanda ya fito daga Ukraine shiga ƙasar.

Wannan lamari dai ya nuna ƙarara yadda ake cin fuskar baƙaƙen fata, duk da cewa yaƙi ake, amma hakan bai hana jami’an Ukraine din nuna musu halin ko in kula ba.

Ofishin jekadancin Najeriya a Poland ya ce ya tura jami’ansa zuwa kan iyakoki domin taimakawa ƴan ƙasar tsallakawa.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *