Sports
FIFA ta haramta wasannin ƙasa da ƙasa a Russia da kuma hana sanya tuta ko yin taken ƙasa

Daga kabiru basiru fulatan
Hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA, ta yanke shawarar cewa ba za a buga gasar kasa da kasa a Russia ba, inda ake gudanar da wasannin gida a filayen wasanni ba mallakar ƙungiyoyi ba sannan ba tare da ‘yan kallo ba.
FIFA ta baiyana hukuncin ta ne a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, bayan da kasashen duniya su ka yi Alla-wadai da mamayar da Russia ta yi wa Ukraine.
Har ila yau, Hukumar ta ce dole ne Russia ta shiga gasar kwallon kafa ta ƙasa da ƙasa da sunan ” Taraiyar Tawogar Ƙwallon Ƙafa ta Russia (RFU)”.
FIFA ta ƙara da cewa ba za a yi amfani da tuta ko taken ƙasar Russia a wasannin da ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na ƙasar ke shiga ba.”
An yi ta kiraye-kirayen a hana tawagar ƴan wasan ƙwallon ƙafar Russia ta maza shiga gasar cin kofin duniya ta 2022 da za a yi a Qatar a watan Nuwamba da Disamba.
Kasashen Poland da Sweden da Jamhuriyar Czech sun ki buga wasa da Russia a gasar cin kofin duniya.