News
Yan sanda sun ceto mutane 7 da aka yi garkuwa da su a Zamfara

Daga Yasir sani abdullahi
Rundunar Ƴan sandan Jihar Zamfara tare da haɗin gwiwar sojojin da aka girke a yankin Dansadau a Ƙaramar Hukumar Maru ta jihar, sun yi nasarar ceto wasu mutane bakwai da aka yi garkuwa da su, ƴan asalin ƙauyen Chibade da ke Ƙaramar Hukumar Rijau ta Jihar Neja.
Da yake gabatar da wadanda abin ya shafa a shelkwatar ƴan sanda ta Zamfara, Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Ayuba Elkana, wands ya samu wakilcin PPRO SP Shehu Mohammed, ya ce wadanda abin ya shafa a yayin zantawa da su sun sanar da ‘yan sanda cewa, a ranar 21 ga Fabrairu, 2022, ‘yan bindiga da dama sun kai farmaki kauyen su (Chibade).
Sun ƙara da cewa ƴan ta’addan sun yi awon gaba da su bakwai daga cikinsu zuwa inda su ka kai su cikin ƙurysr jeji a Dansadau na jihar Zamfara.
A cewar CP Elkana, jami’an hadin gwiwa na ‘yan sanda da na soji, yayin da su ke gudanar da aikin share fage na daji da ke kewayen Dansadau, sun yi nasarar ceto wadanda abin ya shafa tare da kai su asibitin kwararru na Yariman Bakura da ke Gusau inda aka duba lafiyarsu.
Kwamishinan ya ci gaba da cewa, za a mika dukkan wadanda abin ya shafa ga kwamishinan ‘yan sandan jihar Neja domin daukar matakin da ya dace da zarar an kammala binciken da ya dace da nufin ganin sun sake haduwa da iyalansu.
Ya kuma taya wadanda lamarin ya rutsa da su da iyalansu murnar samun ‘yancinsu, ya kuma ba da tabbacin ‘yan sanda za su ci gaba da gudanar da ayyukansu na kawar da ‘yan fashin daji da sace-sace da duk wani nau’i na miyagun ayyuka.