News
Ku kwaikwayi taimakon al’umma a gurin A’isha Buhari, Shugaban NYSC ya shawarci attajirai
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Darakta-Janar na Hukumar Bautar Ƙasa, NYSC, Shuaibu Ibrahim, ya yi kira ga attajirai da kamfanunuwan ƙasar nan da su kwaikwayi irin taimakon al’umma da Uwar gidan Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari ta ke yi.
Ibrahim ya yi kiran ne a yayin rantsar da sabbin ƴan bautar ƙasa rukunin A, rundunar I na 2022 a sansanin horo da ke Ƙaramar Hukumar Ganjuwa, Jihar Bauchi a yau Talata.
Ya yaba wa matar shugaban ƙasar bisa Tallafin magunguna da ta baiwa hukumar NYSC, inda ya ƙara da cewa Tallafin ya taimaka wa ƴan bautar ƙasa a shirin bada magunguna kyauta a cikin ƙauyuka.