News
Jami’an Tsaro sun Murkushe Yan bindiga Sama da 200 a Jihar Neja.

Daga yasir sani abdullahi
Sama da ‘yan ta’adda 200 ne jami’an tsaro suka kashe a jihar Neja cikin kwanaki hudu da suka gabata.
Kwamishinan kananan hukumomi, masarautu da harkokin tsaro na cikin gida, Emmanuel Umar ne ya bayyana haka a lokacin wani taro kan harkokin tsaro a jihar, ya ce kungiyoyin ‘yan bindiga hudu ne ke kai hare-hare a jihar.
Ya Kara da cewa, ‘yan ta’adda da dama sun gudu da raunukan harbin bindiga, inda ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da bayar da sahihin bayanan sirri don baiwa hukumomi damar samun nasara a yakin da ake yi da rashin tsaro.
Umar ya bayyana sunayen Shugaban in kungiyoyin ‘yan fashin kamar haka; Bello Turji, Yellow Janbros, Kachalla Halilu da na Ali Kawaje.
Ya kuma ce jami’an tsaro biyu sun mutu a arangamar da jami’an tsaro Suka yi da ‘yan bindigar.
Kwamishinan ya ce an kwato babura da shanu da dama da kuma bindigu yayin arangamar.
Kazalika ya ce jihar ta sake yin shiri kuma a shirye take ta kawo karshen ta’addanci.
Umar ya amince da goyon bayan jami’an tsaro da al’ummomi da masarautun gargajiya da kuma kafafen yada labarai na goyon bayansu a yakin da ake yi da ta’addanci a jihar.