News
3000 kacal muke sayar da Siminti, diloli da ‘yan kayi nayi ne suke tsauwala jama’a – inji Abdussamad Rabi’u mai kamfanin BUA.

Daga muslim yunus abdullahi
Alhaji Abdussamad Isyaka Rabi’u ya bayyana hakan ne yayin zantawa da manema labaran fadar shugaban kasa jim kadan bayan fitowa daga wata ganawa da yayi da shugaba Buhari a ranar talata da ta gabata.
Ya ce kamfaninsa na BUA baya sayar da siminti sama da Naira 3000 ko 3050 amma sai diloli da ‘yan kasuwa su sauwala wa jama’a…
Ya kuma alakanta matsalar da rashin rage farashin da sauran kamfanonin siminti su ka kiyi.