News
Zan fita daga jam’iyyar PDP kafin karshen watan Maris – Inji Kwankwaso.
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Masana na ganin fitar Kwankwaso daga PDP babbar asara ce ga jam’iyyar
Tsohon gwamnan jihar Kano da ke arewacin Najeriya kuma jigo a jam’iyyar PDP mai hamayya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce zai fice daga jam’iyyar kafin karshen wannan watan na Maris.
Tsohon gwamnan ne ya tabbatar wa BBC Hausa wannan labari, inda ya ce ya yi nisa a shirinsa na komawa jam’iyyar NNPP watau New Nigeria Peoples Party.
Wani makusancin tsohon gwamnan ya ce babu tsari a game da yadda ake tafiyar da sha’anin jam’iyyar ta PDP, lamarin da ya tilasta wa Sanata Kwankwaso tattara kayansa domin ya fice daga cikinta.
A watan jiya ne Kwankwaso ya jagoranci wani gagarumin taro na wasu manyan siyasar kasar karkashin wata kungiya mai suna The National Movement TNM