News
Da yiwuwar mace ta yi gwamna a Kaduna, in ji El-Rufai

Daga aminu usman jibirn
Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya baiyana cewa ya na da yakinin cewa mace za ta yi gwamna a jihar duba da yawan mata.
Da ya ke amsa tambayoyi da ga manema labarai a Kaduna a yau Talata, El-Rufai ya ce mata su na da damar yin gwamna har kashi 50 cikin 100 duba da cewa sune su ka kwashi rabin al’ummar jihar.
El-Rufai, wanda mataimakiyarsa mace ce, Hadiza Balarabe, ya ce gwamnatin sa za ta ci gaba da baiwa mata damammaki daidai da maza.
Ya ƙara da cewa gwamnatin sa na da manyan kwamishinoni mata.
Ya ƙara da cewa shi ya ja ganin baiwa mata dama daidai da maza ya na sa su riƙa yin kwazo, wani lokacin ma sama da mazan.
El-Rufai ya kuma yi kira ga sauran gwamnatocin jiha da su riƙa baiwa mata damammaki, inda ya ce “hakan zai kara ciyar da ƙasar nan gaba”.
Gwamnan ya ce jihar na fatan ta samu nagartacce shugaba da zai ɗora da ga kan kyawawan aiyukan da ya ke yi.