News
2023: Masoyin Tinubu, wanda yai alƙawarin yin tattaki da ga Abuja zuwa Legas ya gudu

Daga aminu usman jibrin
Da alama dai Hussein Lawal, masoyin tsohon Gwamnan Jihar Legas, Bola Tinubu, wanda ya yi alƙawarin yin tafiyar ƙafa tun daga Abuja zuwa Legas, ya gudu.
Tun da fari, Lawal ya yi alƙawarin fara tafiyar ne da ga Ƙofar Birnin Abuja zuwa Filin Tafawa Balewa da ke Legas a yau Laraba, domin ya shawo kan Tinubu ya yarda ya tsaya takarar shugaban ƙasa.
Kamar yadda katin gaiyatar da ya aike wa Kamfanin Daillancin Labarai na Ƙasa, NAN domin ɗaukar fara tattakin, ya nuna, Lawal, haifaffen garin Durun da ke Ƙaramar Hukumar Kabo a Jihar Kano zai fara taka sayyada ɗin ne da misalin ƙarfe 10 na safiyar yau Laraba.
Sai dai kuma har zuwa wannan lokaci, ba a ga ƙeyar Lawal ba.
Haka-zalika wani mai suna Chris Richard ne ya sanya hannu a kan katin gayyatar kuma shi ma a na ta neman sa ba a sake shi ba, inda lambar da a ka rubuta a jikin katin ma an ta buga wa amma a kashe.
Tinubu, Jagoran Jami’yar APC na Ƙasa, ya baiyana aniyar sa ta tsaya wa takarar shugabancin ƙasar nan kuma tuni ka ya sanar da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a ranar 10 ga watan Janairu.
Ya kuma baiyana cewa nan gaba zai sanar da aniyar sa ta tsaya wa takara ga ƴan Nijeriya da kuma dalilan da su ka sanya yanke son ya tsaya.