News
Da yiwuwar tashin farashin kayan abinci a 2022 — AFAN

Daga maryam bashir musa
Ƙungiyar Manoma ta Ƙasa, AFAN, reshen Jihar Oyo, ta baiyana fargabar cewa farashin kayan abinci ka iya yin tashin gwauron zabi a 2022, duba da hauhawar farashin kayan noma.
Shugaban AFAN na jihar, John Olateru, shine ya baiyana fargabar a wata hira da ya yi da Kamfanin Daillancin Labarai na Ƙasa, NAN a Ibadan a yau Laraba.
Olateru ya baiyana cewa manoma sun tashi haiƙan domin yin noma a bana.
Sai dai kuma ya koka da hauhawar farashin kayan noman, inda ya ce hakan zai taɓa harkar noma da kuma sanya tashin farashin kayan gona da a ka girbe.
A cewar sa, farashin magungunan shuka ya ruɓanya har sau uku, haka shi ma taki, inda ya ce kuɗin sharar gona ma ya tashi da ga Naira dubu 5 zuwa dubu 12 zuwa 15 a duk hekta ɗaya.
Ya ƙara da cewa kuɗin noma ma ya yi tashin gwauron zabi, inda hakana, a cewar sa, zai haifar da hauhuwar farashin kayan abinci a bana.
Olateru ya kuma koka da wahalar samun canjin kuɗaɗen waje da kuma samun kuɗaɗen ƙasashen wajen kansu, inda ya ce hakan yanka hana manona shigo wa da kayan noma ƙasar nan.