Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya goyi bayan cire gwamnan Yobe Mai Mala Buni a matsayin shugaban riko na APC kamar yadda gwamnan Kaduna Malam Nasir El Rufai ya bayyana.
A hirar da kafar talabijin ta Channels ta yi da shi ranar Talata, El Rufai ya ce gwamnan Neja Sani Bello ya samu goyon bayan Buhari da kuma gwamnonin APC 19.
Sannan ya ce Buhari ne ya ce a cire gwamnan Yobe Mai Mala Buni.
“Buhari ne ya bayar da umarnin a cire shi kuma aka aiwatar, yanzu gwamna Bello ne ya gaje shi,” kamar yadda El Rufai ya bayyana.
Ya ce Mai Mala Buni wanda ba ya ƙasar zai dawo ne a matsayin gwamnan Yobe amma ba matsayin shugaban jam’iyyar APC ba.