Connect with us

News

Kwastam ta kama buhunhunan naman jaki 1,390 a Jihar Kebbi

Published

on

Spread the love

Hukumar hana fasa ƙwauri a Najeriya ta kwastam ta ce ta kama buhunhunan naman jaki 1,390 da ake shirin yin safararsu a Jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Kwantirolan da ke kula da shiyyar Kebbi, Joseph Attah, ya ce darajar kuɗin naman da suka kama ta kai naira miliyan 42.

“Ɗaya daga cikin waɗanda suka zo da naman ya faɗa mani cewa sai da suka yanka jaki kusan 1,000 kafin su samu wannan yawan naman,” in ji Mista Attah.

Advertisement

Ya ƙara da cewa safarar dabbobin da aka ayyana a matsayin waɗanda ba na ci ba ya saɓa wa sashe na 63 (b) na kundin dokar hukumar.

Social embed from twitter

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *