Sports
Liverpool ta cire Inter duk da rashin nasarar da ta yi

Daga maryam bashir musa
Inter Milan ta kawo karshe wasanni bakwai da Liverpool ta yi a jere a Champions ba tare da rashin nasara ba, amma duk da haka Liverpool ta tsallaka zagayen kusa da dab da nakarshe.
Da jimillar kwallayen da aka ci a wasanni, Liverpool ta tsira da ci 2-1 a wasan da aka yi a filin wasa na Andfield da ke Ingila.
Duk da wata kwallo mai kyau da Lautaro Martinez ya ci Liverpool, hakan bai bai wa Inter damar tsallakawa zagaye na gaba ba, saboda kwallon da Robert Firmino da Mo Salah suka ci a wasan farko da aka yi a Milan.
A cikin minti na 61 ne da fara wasan Amrtinez ya bugawa Alisson kwallon da ta shiga raga daga yadi na 20, kuma ya gaza kama ta.
Kokarin da Inter take na samun damar farke kwallonta a tafi karin lokaci ya zo karshe ne bayan da aka kori tsohon dan wasan Arsenal da Manchester United Alexis minti biyu bayan an ba shi katin gargadin farko.
Liverpool ta yi iya kokarinta na jefa kwallo a wasan amma ba ta samu damar hakan ba, sai dai ta daki tirke sau uku a wasan.
Dan wasan bayan kungiyar Joel Matip ya sanya kai ta daki tirke sai kuma Mo Salah da ya daki tirken sau biyu.
An tsayar da wasan na wasu lokuta a minti 45 farko saboda tawagar likitoci ta bukaci hakan.