News
APC ta maida wa INEC martani, inda ta ce ba za ta fasa yin babban taro ran 26 ga Maris ba

Daga yasir sani abdullahi
Jam’iyar APC ta ce ba ta karya doka ba a kan wasikar da ta aike wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, domin ta sanya idanu a babban taron ta mai zuwa.
Idan Ahmed, Shugaban Matasa na Kwamitin Riƙo na APC ne ya baiyana haka da ya ke hira da manema labarai a Abuja a yau Juma’a.
INEC ta ƙi karɓar takardar da APC ɗin ta aike mata domin gayyatar ta taron gaggawa, a wani mataki na shirin babban taron da za ta yi a ranar 26 ga watan Maris.
INEC ta ce APC ba ta bi ka’ida ba wajen aika wasiƙar.
Sai dai kuma Ahmed ya ce jam’iyar ta bi dukkan wasu ƙa’idoji kafin ta sanar da INEC.
Ya ce Farfesa Tahir Mamman, wanda ya ke jagorantar fannin Shari’a na jam’iyar, zai yi bayani a kan hakan nan gaba kaɗan.