Labarai
Rasha ta ƙwace agogunan ƙasaita na miliyoyin daloli a wasu shaguna

Daga Kabiru basiru fulatan
Jami’ai a Rasha sun rawaito cewa an ƙwace agogunan ƙasaita da kudinsu ya kai na miliyoyin daloli.
Kafar yada labaran kasar ta ce jami’an tsaro ne suka je shagon da aka ajiye agogunan a ranar Talata inda suka zargi cewa an saɓa wa dokokin shige da ficen kaya.
Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan Switzerland ta yi watsi da kiraye-kirayen kasashen yamma na bin sahunsu domin a ƙaƙaba wa Rasha takunkumi saboda mamayar da take yi wa Ukraine.
Agogunan da aka ƙwace na da matuƙar tsada, a inda ake sayar da duk guda ɗaya a kan dala dubu 920.
-
Labarai7 days ago
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Yi Wa Masu Digirin Ƙasashen Waje Jarrabawa
-
Labarai3 days ago
Jami’an Tsaro A Pakistan Sun Kama ’Yan Najeriya 20 Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi
-
Labarai2 days ago
Hare-haren Ta’addanci Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 835 A Najeriya Cikin Wata Guda – Rahoto
