News
Kotu ta umarci a zare ₦300,000 daga asusun kakakin ƴan sandan Kano
Daga Hamza Yusuf Abdulmumin
babbar Kotun tarayya da ke Kano ta bada umarnin a cire Naira dubu ɗari uku da aka samu a asusun banki na mai magana da yawun ƴan sandan Kano SP. Abdullahi Haruna Kiyawa.
Kotun ta ce, idan aka cire kuɗin za a a biya wani matashi Bashir Bashir Galadanci da su.
A shekarar da ta gabata ne Kotun ta umarci Abdullahi Kiyawa da ya biya Galadanci diyyar naira miliyan guda sannan ya shiga kafafen yaɗa labarai ya nemi afuwarsa, saboda ɓata masa suna da yayi.
Sai dai har yanzu Kiyawan bai cika waɗannan umarni ba, abin da ya sanya Galadanci ya sake komawa Kotun inda ta umarci a bincikin asusun bankin Kiyawan, inda aka samu dubu ɗari ukun.
INDARANKA ta so jin ta bakin SP. Kiyawa amma har kawo lokacin da muke haɗa wannan rahoto haƙanmu bai cimma ruwa ba.
-
News7 days ago
An Tsare Kwamandan NSCDC Da Wasu Jami’an hukumar Da A Ke Zargi Da Sakaci A Mutuwar Masu Hakar Ma’adanai 37 A Neja
-
News6 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Ɗalibai 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina
-
News5 days ago
NLC Za Ta Fara Fafutukar Neman Sabon Ƙarin Mafi Ƙarancin Gabanin 2027 — Ajaero
