Wasu rahotanni da ke yawo a shafukan sada zumunta da kuma wasu jaridu a Najeriya na cewa ‘yan bindiga sun sake kai hari a jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja.
Jaridun Najeriya irin su Guardian sun rawaito cewa a karo na biyu cikin awa 24 ‘yan bindiga sun dasa abubuwan fashewa a layukan-dogo lamarin da ya tilasta wa wani jirgin kasa da ya tashi daga Kaduna zuwa Abuja tsayawa ranar Talata.
Sai dai binciken da BBC Hausa ta gudanar ya nuna cewa babu wani jirgin fasinja da ya tashi daga Kaduna zuwa Abuja – illa dai jirgin kasa da Ministan Sufuri ya hau daga Abuja zuwa wurin da aka kai harin ranar Litinin.
Dama dai hukumar lura da jiragen kasa ta Najeriya ta fitar da sanarwa cewa ta dakatar da jigilar jiragen kasa daga Abuja zuwa Kaduna saboda harin da ‘yan bindiga suka kai kan wani jirgin kasa ranar Litinin da daddare.
Harin dai ya yi sanadin mutuwar akalla mutum takwas yayin da fiye da mutum 20 suka jikkata kuma suke jinya a wasu asibitoci da ke Kaduna.
Bayanan da muka samu daga wasu ma’aikatan tashar jingin kasa da ke Kaduna sun tabbatar da cewa jiragen ba su yi aiki ba ranar Talata.
Sai dai hukumomi ba su ce komai a kan rahotannin kai hari a kan jirgin kasan a karo na biyu cikin awa 24 ba.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi tir da kai harin kana ya bukaci jami’an tsaro su karfafa ayyukansu na kare rayukan ‘yan kasar.

