Labarai
Kayan yaƙi da hukumomin Najeriya suka kama a Legas.

Daga maryam bashir musa
Hukumar yaƙi da fasa ƙwauri ta Najeriya da ke tashar jiragen sama shiyyar NAHCO a birnin Legas ta kama tufafin sojoji masu yawa da ƙananan jiragen leƙen asiri na yaƙi marasa matuƙa masu yawa.
Konturola Sambo Kayilil Dangaladima mai kula da shiyyar hukumar kwastam a tashar jiragen sama ta Murtala Muhammad ne ya bayyana wa manema labarai hakan.
Akwai kuma ƙwayar Tramadol ta sama da naira biliyan biyu da kuma wani ganyen shayi mai fitar da hankali da ake zargi an shigo da shi Bangladesh da kuma kusa da wani sashe na Saudiyya.
Hukumar kwastom ta hannunta wadannan makaman da kakin soje ga rundunar sojen Najeriya da kuma kwayoyi a hannun hukumar yaki da shan miyagun kwayoyi da kuma hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta NAFDAC.
A wani labarin kuma…
Hukumar hana sha da fataucin miagun kwayoyin ta Najeriya (NDLEA), ta ce ta kama wasu masu ikirarin bokanci, wadanda ake zargin suna cikin wata kungiya da ke safarar miyagun kwayoyi ta jirgin sama na Murtala Mohamed da ke Lagos.
Kakakin hukumar ta NDLEA na kasa Femi Babafemi ya sanar da cewa wadanda aka kama a filin jirgin na Lagos suna dauke da kwayoyi samfurin TRAMADOL sama da miliyan ɗaya da rabi da kuma makudan kudade, kuma an kama su ne a cikin wannan wata na Maris.
-
Labarai6 days ago
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Yi Wa Masu Digirin Ƙasashen Waje Jarrabawa
-
Labarai2 days ago
Jami’an Tsaro A Pakistan Sun Kama ’Yan Najeriya 20 Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi
-
Labarai6 days ago
An Kashe Mutane 418, An Yi Garkuwa Da 227 Cikin Watanni Biyu A Nijeriya — Rundunar Ƴansanda
