Connect with us

News

Sarkin Musulmi ya umarci a soma duba sabon watan Ramadan

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan

 

 

Sarkin Musulmi, Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar wanda shi ne shugaban majalisar koli kan harkokin addinin Musulunci ta Najeriya, ya buƙaci al’ummah Musulmi su soma duba sabon watan Azumin Ramadana.

Wannan na kunshi cikin wata sanarwa da ya fitar dauke da sa hannun babban jami’i a majalisar, Arc. Zubairu Haruna Usman-Ugwu.

Sanawar ta umarci Musulmi su soma duba sabon watan daga yammacin Juma’a 1 ga watan Afrilun, 2022, wanda ya yi daidai da 29 ga watan Sha’aban shekara ta 1443 bayan hijira.

Idan aka yi nasarar ganin watan a gobe Juma’a to za a tashi da Azumi ranar Asabar a matsayin 1 ga watan Ramadana kenan. Idan kuma ba a ga wata ba to 1 ga watan Ramadan zai kasance Lahadi 3 ga watan Afrilu, a cewar sanarwar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending