Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya ce zai gana da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari bayan harin da ‘yan fashi suka kai wa jirgin ƙasa na Kaduna zuwa Abuja.
El-Rufai ya bayyana hakan yayin da ya kai ziyarar jaje ga mutanen Ƙaramar Hukumar Giwa ta jihar bayan hare-haren ‘yan bindiga a makon da ya gabata da ya kashe fiye da mutum 50 a yankin.
“Ba wai gwamnati ba ta san abin da ke faruwa ba ne, muna sane. Kawai dai wasu ne da ya kamata su ɗauki mataki har yanzu ba su yi hakan ba,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa “za mu ci gaba da matsa wa shugaban ƙasa da jami’an tsaro don su ɗauki mataki”.

