News
Rushewar ginin wani masallacin juma’a a Nguru dake jihar Yobe
Rushewar ginin wani masallacin juma’a a Nguru dake jihar Yobe, ya hallaka kimanin mutane 4, tare da raunata da dama.
Adadin zai iya karuwa, yayinda yan agaji ke cigaba da laluben gawarwaki.
A kwana kin baya ne dai, shugaban darikar tijjaniya na kasar nan, Mallam Muhammadu Sanusi II, ya je jihar Yoben, domin aza harsashin ginin masallacin, wanda akayiwa lakabi da Madinatu Kaulaha.
Mabiya darikar tijjaniya daga sassan kasar nan har da makobtan kasashe ne ke halartar aikin ginin, domin neman tabarraki.
Zai kasance na biyu mafi girma a fadin jihar, bayan babban masallacin jiha dake Damaturu.
-
News7 days ago
An Tsare Kwamandan NSCDC Da Wasu Jami’an hukumar Da A Ke Zargi Da Sakaci A Mutuwar Masu Hakar Ma’adanai 37 A Neja
-
News6 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Ɗalibai 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina
-
News5 days ago
NLC Za Ta Fara Fafutukar Neman Sabon Ƙarin Mafi Ƙarancin Gabanin 2027 — Ajaero
