Connect with us

News

Watan Ramadan Watane Na Daban Da Sauran Watanni-Khadija Abdullahi Muhmud

Published

on

Daga Khadija Abdullahi Muhmud

Watan Ramadan watane na daban da sauran watanni,musanman ta Hanyar bambanta cima da kuma abubuwan da ya kamata mu dinga sha a lokutan Sahur da kuma buda baki.

A lokacin watan Ramadan ya kamata ace mu dinga ci da shan abubuwan da zasu taimakawa jikinmu wajen dawo da ku zarin a jikin mu.

Cin abubuwan masu Gina jiki kamar kayan marmari da kuma abubuwan masu ruwa-ruwa. Ga iyayen mu mata da suke da juna-biyu yana da kyau su dinga amfani da kabewa da kuma gwanda da kayan ganye.

Yin duk wani aiki da mukasan zamuyi kafin kwallewar rana da kuma Sanin irin ayyukan da zamuyi a wannan watan domin infanta lafiyarmu.

Ga wadanda ya zamar musu dole sai sun shiga rana yana da kyau su yawaita amfani da kayan marmari suma kamar dai iyayen mu masu juna biyu domin bawa jikinsu gudunmawar rike ruwa don gudun wahala.

Advertisement

A wannan watan kula da kai abune mai mahimmanci don gudun Samarwa kai matsala musamman wasu maza da ya zama dole sai sun fita rana domin gudanar da ayyukansu.

Ga Matan da Duke zaune a cikin gida ya kamata su kula da yaushe ne ya kamata su dinga ayyukansu,domin yana da kyau mace ta lura sosai wajen rage mafi yawan ayyukansu kafin lokacin da rana zatayi zafi daga nan sai su jinkirta zuwa lokacin da rana tayi sanyi yin haka zai taimakawa lafiyar kowa da kowa.

Kula da kananan yara,wadanda zasu iya azumin da kuma wadanda ba zasu iya ba,domin a wasu lokutan akwai yaran da zakaga sun jajirce sai sunyi azumi Wanda zai kai ga Samar musu da matsala. Saboda haka yana da kyau a lura da wadanna yara ne za su iya azumi da ma wadanda ba zasu iya ba da kuma kula da basu ruwa sosai lokacin da aka sha ruwa wato buda baki dakuma basu abinci mai kara lafiya a jikin dan Adam.

A wasu lokutan akwai mutanen da suke da dabi’ar saka kankara a Kansu had su kulle kannasu to wannan babbar hanyace ta cutar da kai.
Domin yana gaggawar kawowa kowane Dan Adam matsala a lafiyarsa musamman ido da kuma kai.

Daga karshe ina fatan zamuyi wa kasa da kuma iyayen mu maza da mata da abokan mu da yan,uwan musulmi baki daya addu,a dan samun nassara a wannan wata mai albarka.
Allah yasa muna daga cikin wanda ake gafartawa a wannan watan mai albarka.

Ya Allah ka bamu ikon bauta maka yadda ya kamata,Allah ka amshi ibadunmu,ka yafe mana zunuban mu,ka shiryar damu,kuma ka zaunar da kasarmu lafiya,domin darajar wannan wata mai Albarka #ramadanmubarak🌙 #ramadankareem

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending