‘Yan bindiga sun kashe aƙalla mutum 17 a wasu hare-hare da suka kai kauyuka hudu da ke karamar hukumar Anka ta jihar Zamfara.
Mazauna yankunan sun ce ‘yan bindigar sun bude wuta kan mai uwa-dawabi a kauyen Kadaddaba da tsakar rana.
Rahotanni na cewa sun isa kauyukan ne akan babura suka buɗe wa mutane wuta lokacin da suke fitowa daga masallaci bayan sallah Azahar.
Har yanzu dai rundunar ‘yan sanda ba su yi tsokaci ba kan hare-haren.
