Connect with us

Labarai

Za a tura ƙarin jami’an tsaro kan hanyar Abuja-Kaduna

Published

on

Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta ce za ta tura ƙarin dakaru don kyautata tsaro a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Matakin ya biyo bayan hare-haren da ‘yan bindiga suka kai kan jirgin ƙasa, inda suka kashe mutum aƙalla takwas da raunata wasu 41 sannan suka sace wasu da dama a yammacin Litinin da ta gabata.

Wani saƙo ɗauke da hotuna da mai magana da yawun rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya wallafa a shafinsa na Twitter ya nuna dakarun jere a kan layi.

“Dakaru sun shirya tsaf don tura su aiki na musamman a kan hanyar Abuja-Kaduna. Ana yi musu jawabi a hedikwatar ‘yan sanda ta ƙasa kafin su fita a yau (Asabar),” in ji Mista Adejobi.

Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya Usman Alkali Baba ya kai ziyara wurin aikin da ake yi na gyara layin dogon da ‘yan bindigar suka ragargaza da bam a harin na ranar Litinin.

Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya ce ‘yan Boko Haram ne da haɗin gwiwar ‘yan fashin daji

Advertisement

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending