News
Bayan korarsa daga Masallacin APO an naɗa Sheikh Nura Khalid Limanci a Sabon Masallaci.
Daga kabiru basiru fulatan
Jim kadan bayan ayyana korar Sheikh Nura Muhammad Khalid daga limanci a masallacin APO dake Abuja, rahotanni na tabbatar da cewa an nada malamin a matsayin babban limami a wani masallaci na daban a birnin tarayyar.
Cece-kuce ya barke a Najeriya bayan dakatar da malamin daga limanci sakamakon caccakar gwamnatin tarayya kan matsalar tsaro da ta addabi yan kasar musamman yankin Arewa.
Saidai jim kadan bayan korarsa an nada malamin a matsayin babban limamin wani sabon Masallacin Juma’a dake bayan rukunin gidajen babban bankin kasa CBN dake Abuja.
Rahotanni sun tabbatar da cewar Sheikh Nura Khalil zai jagoranci sallar Juma’a mai zuwa a masallacin da aka bashi limanci.
Advertisements
