Connect with us

News

Jam’iyyun Siyasar Najeriya Za Su Iya Fara Tsayar Da Ƴan Takara Daga Yau, Cewar Hukumar Zaɓe Ta Kasa (INEC)

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan

 

 

Hukumar zaɓen mai zaman kanta a Najeriya ta ce jam’iyyun siyasa da ke son shiga babban zaben 2023 za su iya fara gudanar da zaben fitar da gwani a hukumance.

Hukumar ta ce daga yau 4 ga wannan watan zuwa 3 ga watan Yunin 2022 aka keɓe domin jam’iyyun siyasa su gabatar da zaɓukan cikin gida tare da warware dukkan wani rikici da ka iya tasowa sakamakon zaɓukan.

Jami’a a hukumar zaɓen Hajiya Zainab Aminu Abubakar ta ce lokacin da aka ware na fitar da ƴan takara na cikin kundin dokokin zaɓe na ƙasar.

Advertisement

Ana son jam’iyyun siyasar su tsayar da ƴan takara tare da warware duk wani saɓani kafin cikar wa’adin da aka ƙayyade.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending