News
Kungiyar Dattawan Arewa ta yi fatali da Kudirin Gwamnan El-Rufa’i
Daga kabiru basiru fulatan
Kungiyar Dattawan Arewa wato ACF ta yi fatali da Kudirin Gwamnan Nasir El-Rufa’i na jihar Kaduna kan kawo Sojojin haya idan gwamnatin Tarayya ta gaza shawo kan matsalar tsaron da kasar nan ke fuskanta.
El’rufai yayi wannan iƙirarin ne tun bayan ta’azzarar hare-haren Yan bindiga a jihar Kaduna, ciki har da na ranar Litinin din data gabata inda farmaki Yan bindiga kan jirgin kasa da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna ya hallaka Mutum 9 tare da awon gaba da akalla mutum 21.
Kazalika a cikin wata sanarwa da Sakataren Kungiyar Murtala Aliyu ya fitar a jiya Lahadi, ya ce shawo kan matsalar tsaro ya rataya ne a wuyan gwamnatin Tarayya don haka akwai bukatar a kwantar da hankula wajan lalubu hanyoyin da za’a warware matsalar.
A cewar sanarwar, gayyatar sojojin kasashen waje ko sojojin hayar, “dole ne a yi taka-tsan-tsan kan irin wannan mataki.
-
News7 days ago
An Tsare Kwamandan NSCDC Da Wasu Jami’an hukumar Da A Ke Zargi Da Sakaci A Mutuwar Masu Hakar Ma’adanai 37 A Neja
-
News5 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Ɗalibai 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina
-
News5 days ago
NLC Za Ta Fara Fafutukar Neman Sabon Ƙarin Mafi Ƙarancin Gabanin 2027 — Ajaero
