Connect with us

News

Osinbajo ya sanar da zai tsaya takarar shugaban ƙasa a 2023

Published

on

Daga Kabiru basiru fulatan

 

 

 

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo ya ƙaddamar da takarar shugabancin ƙasar nan a 2023.

Osinbajo ya sanar da zai tsaya takarar ne a wani gajeren saƙo da a ka yaɗa a Channels TV, bayan an shafe watanni a na raɗe-raɗi.

Advertisement

“Ina mai sanar da ku cewa zan tsaya takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyar APC.

“Idan an zaɓe ni, zan bada damar harkokin kasuwanci su bunƙasa. Zan bar ma’aikatun gwamnati su riƙa gudanar da harkoki sannan zan bunƙasa shirin tallafa wa ƴan ƙasa domin kammala aikin nan na fitar da ƴan Nijeriya miliyan 100 da ga ƙangin talauci.

“Sabo da haka ina neman haɗin kan duk wani ɗan ƙasa domin mu haɗu mu ciyar da ƙasar nan gaba,” in ji shi.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending