News
Farashin Zobo yayi tashin gwauron zabi a Kano.
Yayinda aka shiga rana ta 12 a watan azumin Ramadhana rahotanni na tabbatar da farashin Zobo yayi tashin gwauran zabi a jihar nan.
Farashin na Zobo dai ya karu da sama da naira dubu 10 a buhu guda kamar yadda wani dan kasuwa a kasuwar Gama dake karamar hukumar Nasarawa ya bayyana.
Dan kasuwar mai suna Ahmad Dan Sokoto ya shaidawa wakilinmu Qaribullah Abdulhamid Namadobi cewar kayan masarufi na karuwa, amma abinda yafi tsada shine Zobo inda ake saida buhunsa naira dubu 52 sabanin Dubu 36 da ake sayarwa a baya.
Karuwar farashin na Zobo dai baya rasa Nasaba da yadda bukatarsa ke karuwa a watan Ramadhana.
Kafin zuwan azumi dai malaman addinin musulunci sunyi kiraye-kirayen saukakawa alumma farashi.
To saidai daga bayanan dake futowa daga kasuwanni a Kano ana samun karin farashin kayan masarufin, kuma alumma na cigaba da kokawa da tsadar da suke fuskanta a wannan lokaci na azumin Ramadana
