Connect with us

Labarai

Mai neman shugabancin kasar Nigeria yace a shekara hudu zai canza tattalin arzikin kasarnan

Published

on

Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Daga khadija Abdullahi Mahmud.

 

 

Sanata Orji Uzor Kalu ya ce a cikin shekaru hudu kacal zai iya rikidar da tattalin arzikin kasar nan.

 

Orji Uzor Kalu ya yi alkawarin cewa karfin tattalin Najeriya zai zama kamar na Amurka da Jafan.

Advertisement

‘Dan takarar Shugaban kasar ba zai nemi tuta idan ba yankin shi APC ta kai takara a zaben 2023 ba.

Sanata Orji Uzor Kalu ya cika baki cewa karfin tattalin arzikin Najeriya zai bunkasa a cikin shekaru hudu muddin ya zama shugaban kasa.

 

PM News ta rahoto shugaban masu tsawatarwa a majalisar dattawan ya na wannan alkawari a lokacin da ‘yan jarida suka yi hira da shi a garin Abuja.

 

A cewar Orji Uzor Kalu, karfn GDP na Najeriya zai zama tamkar na Amurka, Jafan da sauran manyan kasashen Duniya, idan ya karbi shugabanci.

Advertisement

“Zan iya canza tattalin arzikin Najeriya a shekaru hudu, zan maida karfin jimillar tattalin arzikin mu ya rika takara da na Amurka, Jafan da sauransu.”
“Kowa yana cewa shi ‘dan takara ne, aikin me suka taba yi? Me suka yi wa jama’a? Sun iya kafa mutane? Ni na dauki mutane 13, 000 aiki a Najeriya.”
Na cancanci gaje kujerar Buhari: Inji Amaechi ga jama’ar Katsina yayin wata ziyara
“Kuma ina da karfin da zan iya jagorantar mutane.” Sanata Orji Uzor Kalu
Zan yi takara idan …
People Gazette ta rawaito ‘Dan majalisar yana cewa zai nemi takara ne da sharadin cewa mutumin kudu maso gabas aka yarda za a ba tikitin jam’iyyar APC.

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending