Connect with us

News

Hauhawar farashin kayayyaki ta ƙaru a Najeriya a watan Maris

Published

on

Daga yasir Sani abdullahi

 

Kayan kasuwa

Hauhawar farashin kayayyakin da mutane ke saya a Najeriya wato Cosumer Price Index (CPI) ta ƙaru zuwa kashi 15.92 cikin 100 a watan Maris na 2022, yayin da ake fama da tashin farashin kayan abinci a ƙasar.

Adadin shi ne mafi girma da aka samu tun Oktoban 2021, wanda kuma ya ƙaru da kashi 0.22 a kan 15.7 cikin 100 da aka samu a Fabarairun 2022.

Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ce ta bayyana hakan cikin rahoton da ta fitar ranar Juma’a.

Sai dai rahoton ya nuna cewa ɗaukacin hauhawar farashi a ƙasar ya ragu daga kashi 14.01 cikin 100 a watan Fabarairu zuwa 13.91 a watan Maris.

NBS ta ɗora alhakin tashin farashin kayayyakin kan tashin farashinn kayayyaki kamar gas da tufafi da kayan tsafta.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending