Labarai
Ni takarar shugaban ƙasa zan tsaya, ba zan yarda da toshiyar bakin mataimakin shugaban ƙasa ba — Wike
Advertisements

Daga kabiru basiru fulatan
Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike, mai neman takarar shugaban kasa, ya ce ba zai yarda da a bashi toshiyar bakin takarar mataimakin shugaban kasa ba.
“Ban fito don don na sasanta da wani na zame masa mataimaki a takara ba. Ni na fito ne domin in tsaya takarar shugaban ƙasa,” in ji Wike, wanda ya shaida wa shugabannin jam’iyyar a Benin a jiya Alhamis.
Aike ya koka da yadda yanayin rashin tsaro ya mamaye kasar, yana mai cewa akwai bukatar Nijeriya ta kashe makudan kudade wajen tattara bayanan sirri domin dakile taɓarɓarewar tsaro.
Gwamnan na PDP ya bayyana cewa ɗaya daga cikin manyan batutuwan da ke haddasa rashin tsaro da ake fama da shi a kasar nan shi ne gazawar Gwamnatin Tarayya wajen kashe isassun kudade domin tattara bayanan sirri kan dakile matsalar tsaro.
“Akwai bukatar kashe isassun kudade wajen nemo da bayanan sirri don dakile rashin tsaro a kasar. Ba ku jira don ƙyale abubuwan da suka faru su faru ba kafin ƙoƙarin magance su. “
Wike ya bayyana cewa, ka’idojin farko da kowane shugaban kasa zai yi nasara a Najeriya shi ne yadda irin wannan shugaban zai iya tabbatar da tsaron kasa da kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa.
Advertisements
-
Labarai7 days ago
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Yi Wa Masu Digirin Ƙasashen Waje Jarrabawa
-
Labarai3 days ago
Jami’an Tsaro A Pakistan Sun Kama ’Yan Najeriya 20 Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi
-
Labarai2 days ago
Hare-haren Ta’addanci Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 835 A Najeriya Cikin Wata Guda – Rahoto
