Akalla mutane 35 suka mutu sannan 71 suka jikkata a Zimbabwe yayin da wata motar bas dauke da Kiristoci da ke kan hanyarsu ta zuwa coci domin yin bikin Easter ta kauce kan hanyarta inda ta fada wani rami, a cewar ‘yan sanda.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito cewa motar tana dauke da mambobin cocin Christian Church wadanda ke kan hanyarsu ta zuwa wani taron Easter a kudancin kasar.
“Zan iya tabbatar muku cewa hatsarin ya faru ne jiya da daddare. Kawo yanzu mutane 35 sun mutu sannan 71 sun jikkata,” a cewar mataimakin Kwamishin ‘yan sanda Paul Nyathi a hirarsa da AFP.
“Alamu sun nuna cewa an yi wa motar lodin da ya wuce kima,” in ji shi.
Galibin motocin bas a Zimbabwe suna daukar mutane 60 zuwa 75.
“A matsayinsu na mabiya addinin Kirista, ya kamata su zama abin misali amma sai suka yi tafiya da daddare abin da ba a so,” a cewar Nyathi.
