Connect with us

News

An ba Saddiq Musa Kaita Sarautar Sardaunan Katsina

Published

on

Daga Khadija abdullahi muhd

 

 

Advertisement

 

Sarkin Katsina Dr Abdulmuninu Kabir Usman ya tabbatar wa Saddiq Musa Kaita da sarautar Sardaunan Katsina.

Advertisement

Sarkin Katsina ya tabbatar masa da sarautar ne a cikin wata takarda mai ɗauke da sa hannunsa a ranar Asabar 16 ga watan Afrilu.

“Na amince da ba ka Sarautar Sardaunan Katsina kamar yadda ka nema,” kamar yadda Sarkin Katsina ya bayyana a cikin takardar.

Advertisement

Sanarwar ta ce nan gaba za a sanar da ranar bikin naɗin nasa.

Saddik jika ne ta bangaren uba ga sarkin Fadan Katsina Isma’ila Damale wanda shi kuma ɗa ne ga Wazirin Katsina na farko Haruna Kaita.

Advertisement

Haka kuma ta bangaren uwa jika ne ga Makaman Katsina Marigayi Tukur Idris Nadabo hakimin Bakori.

A kwanakin baya ne aka ba Ibrahim Ida sarautar Wazirin Katsina wanda a baya shi ne Sardaunan Katsina.

Advertisement

Wannan na zuwa ne bayan ajiye sarautar waziri da Alhaji Sani Lugga ya yi saboda wasu dalilai.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending